ABNA24 : Rahotannin sun ce Farfesa Dahiru Yahaya wanda ya kasance tsohon malami ne da yayi koyarwa a jami’oin Bayero da ke Kano (BUK) da kuma Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya ya rasu ne a yau din nan Laraba a wani asibiti a Kanon bayan dan gajeren rashin lafiya.
Wasu kafafen watsa labarai sun jiyo daya daga cikin ‘yan’uwan marigayi Farfesa Dahiru Yahayan, wato Bashir Habib Yahaya yana cewa a yammacin yau din ne dai za a yi wa marigayi salla da kuma bisne shi kamar yadda dokokin addinin Musulunci suka tanada a gidansa da ke Ungogo da ke Kanon.
Malam Bashir ya kara da cewa marigayin ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kuma ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya ashirin da biyu da kuma jikoki da dama.
Baya ga koyarwa a jami’oi har ila yau kuma Farfesa Yahaya yayi rubuce-rubuce kan batutuwa daban-daban bugu da kari kan lakcoci daban-daban da ya dinga gabatarwa.
Daga cikin lakcocinsa da suka dau hankula har da wadanda ya gabatar a lokuta mabambanta a Husainiyar Baqiyatullah ta harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakub El-Zakzaky haka nan kuma da shaidar da ya bayar a wajen kwamitin binciken da aka kafa don binciko abin da ya faru a Zariya a shekara ta 2015 bayan harin da sojoji suka kai wa 'yan harkar Musuluncin.
342/